Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da taron karawa juna sani a birnin Qum na shahadar jagoran gwagwarmaya Sayyid Hasan Nasrallah (RA) karkashin kulawar Mu’assasa As-Sadiq, inda daliban Jami’ar Zahra da Bint al-Huda da daliban Jami’ar Al-Mustafa da malamai suka halarta.
Hujjatul Islam Sayyid Murad Reza Rizvi da Hujjatul Islam Sayyid Mujtaba Sayyid Soleimani ne suka gabatar da jawabai a taron karawa juna sani da kuma jinjinawa Sayyid na gwagwarmaya da shahidan gwagwarmaya a cikin jawabansu, inda suka jaddada cewa shahadar Sayyid Hasan Nasrallah ya kara karfafa azama da tsayin daka ga al'ummar musulmi.
A lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta Abna News Hujjatul Islam Sayyid Shahzad Reza shugaban gidauniyar Al-Sadiq ya godewa daukacin dalibai da malamai da kuma Kamfanin Labaran ABNA. Ya ce a wannan karon yana da matukar muhimmanci a gare mu mu bayyana sakon gwagwarmaya ga duniya, domin wannan shi ne babban nauyi da ke kan mu awannan lokacin.
Hujjatul Islam Sayyid Shahzad Reza ya kara da cewa babbar manufar Mu’assasa ta Al-Sadiq Qom ita ce gabatar da tunanin Imam Khumaini ga duniya da kuma yada akidar Wilayatul-Faqih da yada muryarta a duk fadin duniya.












Your Comment